Jigawa Online News | Labaran Jigawa
🗓️ Talata, 6 Oktoba 2026 • Labaran Jigawa a kullum

Jigawa Online News

Gidan labaran Jihar Jigawa
⚡ SABON LABARI
Ku kasance tare da Jigawa Online News domin samun sabbin labarai daga kananan hukumomi 27 na Jihar Jigawa.
Jaridu da labarai
LABARAI

Jigawa Online News: Sabbin labarai daga sassan Jihar Jigawa

Jigawa • Yau, 10:30 na safe
Siyasa
SIYASA

Sabbin abubuwa a fagen siyasar Jigawa

Sa'o'i 2 da suka wuce
Ci gaban gari
RUWASA

Rahoto kan ayyukan raya karkara da birane

Sa'o'i 4 da suka wuce
Labaran yau
LABARAI

Abubuwan da suka fi daukar hankali yau

Jiya

Sabbin Labarai

Duba duka →
News
JIGAWA

Sabbin abubuwan da ke faruwa a fadin Jihar Jigawa

Rahoto na musamman daga sassan jihar.

Yau • 09:15
Community
AL'UMMA

Engr. Sidi foundation. Al'umma sun bayyana ra'ayinsu kan ci gaban yankinsu

Labari da bayanai daga jama'a.

Yau • 08:40
Office
HARKOKIN JIHA

Sabbin shirye-shiryen bunkasa ayyukan jama'a

Bayani kan shirye-shiryen ci gaba.

Jiya • 17:20
Technology
FASAHAR ZAMANI

Fasaha na taimakawa wajen yada labarai cikin sauri

Yadda kafafen zamani ke sauya aikin jarida.

Jiya • 15:05

🚰 Labaran Ruwasa

Duba duka →
Noma
RUWASA

Rahotanni daga manoma da al'ummomin karkara

Bayanan rayuwar jama'a da ayyukan karkara.

Ruwa
RUWA

Rahoto kan samun ruwa da muhalli a Jigawa

Labaran da suka shafi ruwa, muhalli da tsafta.

🏛️ Siyasar Jigawa

Duba duka →
Politics
SIYASA

Sabbin bayanai daga fagen siyasar Jihar Jigawa

Rahotanni da sharhi kan harkokin siyasa.

Meeting
SIYASA

Abubuwan da ke faruwa a jam'iyyu da al'umma

Sabbin labarai da bayanai masu muhimmanci.

📸 Hotuna

Duba gallery →

📱 Sada Zumunta

JIGAWA ONLINE NEWS: GWAMNA BADARU ABUBAKAR YA KAI ZIYARAR TA'AZIYYA KANYA BUBBA.

Sunday, 25 September 2016

GWAMNA BADARU ABUBAKAR YA KAI ZIYARAR TA'AZIYYA KANYA BUBBA.


Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar (MON, mni) a yau ya tafi garin Kanya Babba dake Ƙaramar Hukumar Babura domin ta'aziyyar matasa goma sha biyu da suka rasa rayukansu.

Matasan sun rasu ne sanadiyyar haɗarin mota da ya rutsa dasu a hanyar su ta zuwa Jihar Legas, bayan Bikin Babban Sallah.

Gwamna Muhammad Badaru ya je ta'aziyyar ne a fadan Maigirma Hakimin Kanya Babba kuma Makaman Ringim Alhaji Muhammadu Ibrahim.

Gwamna Badaru yace rasa waɗannan matasa abun alhini ne, kuma ba wai rashi ne ga al'umar Kanya Babba ko Ƙaramar Hukumar Babura kaɗai, yace babban rashi ne ga ɗaukacin al'umar Jihar Jigawa.

Gwamnan yace yana kyautata zaton mamatan suna cikin rahama, saboda sun rasa rayukansu ne a madaidaiciyar hanya, ta neman halak.

Gwamna Badaru yayi addu'ar Allah ya jikan mamatan, ya kuma bawa waɗanda suka samu raunuka lafiya, ya kuma bawa iyalan mamatan haƙurin jure wannan Babban Rashi.

A jawabinsa, Maigirma, Makaman Ringim kuma Hakimin Kanya Babba Alhaji Muhammadu Ibrahim ya godewa Maigirma Gwamnan da wannan ziyarar ta'aziyyar da ya zo musu, inda yace wannan hali ne na Shugaban da ya damu da al'umar sa.

A nan Hakimin yayi addu'ar Allah ya maida Maigirma Gwamnan da ƴan tawagar sa gida lafiya, ya kuma basu ladan ta'aziyya.

Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
25/09/2016

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home