Jigawa Online News | Labaran Jigawa
🗓️ Talata, 6 Oktoba 2026 • Labaran Jigawa a kullum

Jigawa Online News

Gidan labaran Jihar Jigawa
⚡ SABON LABARI
Ku kasance tare da Jigawa Online News domin samun sabbin labarai daga kananan hukumomi 27 na Jihar Jigawa.
Jaridu da labarai
LABARAI

Jigawa Online News: Sabbin labarai daga sassan Jihar Jigawa

Jigawa • Yau, 10:30 na safe
Siyasa
SIYASA

Sabbin abubuwa a fagen siyasar Jigawa

Sa'o'i 2 da suka wuce
Ci gaban gari
RUWASA

Rahoto kan ayyukan raya karkara da birane

Sa'o'i 4 da suka wuce
Labaran yau
LABARAI

Abubuwan da suka fi daukar hankali yau

Jiya

Sabbin Labarai

Duba duka →
News
JIGAWA

Sabbin abubuwan da ke faruwa a fadin Jihar Jigawa

Rahoto na musamman daga sassan jihar.

Yau • 09:15
Community
AL'UMMA

Engr. Sidi foundation. Al'umma sun bayyana ra'ayinsu kan ci gaban yankinsu

Labari da bayanai daga jama'a.

Yau • 08:40
Office
HARKOKIN JIHA

Sabbin shirye-shiryen bunkasa ayyukan jama'a

Bayani kan shirye-shiryen ci gaba.

Jiya • 17:20
Technology
FASAHAR ZAMANI

Fasaha na taimakawa wajen yada labarai cikin sauri

Yadda kafafen zamani ke sauya aikin jarida.

Jiya • 15:05

🚰 Labaran Ruwasa

Duba duka →
Noma
RUWASA

Rahotanni daga manoma da al'ummomin karkara

Bayanan rayuwar jama'a da ayyukan karkara.

Ruwa
RUWA

Rahoto kan samun ruwa da muhalli a Jigawa

Labaran da suka shafi ruwa, muhalli da tsafta.

🏛️ Siyasar Jigawa

Duba duka →
Politics
SIYASA

Sabbin bayanai daga fagen siyasar Jihar Jigawa

Rahotanni da sharhi kan harkokin siyasa.

Meeting
SIYASA

Abubuwan da ke faruwa a jam'iyyu da al'umma

Sabbin labarai da bayanai masu muhimmanci.

📸 Hotuna

Duba gallery →

📱 Sada Zumunta

JIGAWA ONLINE NEWS: GWAMNA MUHAMMAD BADARU YACE BA DON MUZGUNUWA WANI AKE TANTANCE MALAMAN MAKARANTUN FIRAMARE BA...

Wednesday, 3 August 2016

GWAMNA MUHAMMAD BADARU YACE BA DON MUZGUNUWA WANI AKE TANTANCE MALAMAN MAKARANTUN FIRAMARE BA...




Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar (MON, mni) ya karbi bakuncin Shugabancin Gamayyar Kungiyoyin Matasan Jam'iyyar APC na Kananan Hukumomi 27 na Jihar Jigawa.
Kwamared Saleh Birniwa wanda ya jagoranci tawagar a matsayinsa na Shugaban Gamayyar Kungiyoyin yace sun kawo ziyarar ne domin taya Maigirma Gwamna murnar nasarar da ya samu a shekara guda da ya samu yana mulkin Jihar Jigawa, tare da jaddada goyon bayan su da hadin kansu ga Gwamnatin na Maigirma Gwamna.

Kwamared Birniwa ya yabawa irin matakan da ya dauke na tsantseni da sanya ido a dukiyar al'umar Jihar domin kai bantenta tsakanin takwarorinta, wanda shine dalilin da yasa Ma'aikatan Jihar ke samun albashinsu akan kari, tare da cigaba da ayyukan raya kasa, musamman ayyukan tituna da ake yi a fadin Jihar, wanda haka ne ma yasa ake kiran sa da "Baba Mai Kwakuleta".

Kwamared Saleh Birniwa yayi kuma kira ga Maigirma Gwamnan da ya duba irin hanyoyi da aka bi na daukan malaman makarantun firamare a gwamnatin da ta shude, duba da korafe korafen da aka samu, wanda ya janyo aikin da ake yi a halin yanzu na tantance Malaman bangaren. A karshe, Shugaban ya godewa Maigirma Gwamnan na fadada hanyoyin bunkasa tattalin arzikin Jihar da samar da kyakkyawan tsari ga masu zuba jari a cikin Jihar.

A jawabinsa, Maigirma Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana farin cikin sa ga wannan muhimmiyar ziyara da aka kawo masa, inda yace ziyarar na 'yan cikin gida ne wanda suke da ruwa da tsaki a samuwar gwamnatin.
Gwamna Badaru ya bayyana cewa Gwamnatin sa tana iya kokarinta na farfado da harkokin tattalin arzikin Jihar da kuma kulawa na musamman da take baiwa bangarorin Ilimi da na lafiya.
Gwamnan ya kara da cewa ayyukan tantance malaman makarantun firamare da ake yi a halin yanzu ba wai domin musguna wani ake yi ba, sai don karfafa bangaren.

A karshe Gwamna Muhammad Badaru ya yabawa musu da irin hakuri, juriya da fahimta da irin kokarin da suke yi na wayar da kan al'uma halin da gwamnati ta tsinci kanta a ciki na tabarbarewar tattalin arziki da kuma irin matakai da ake dauka na shawo kan lamuran, inda ya tabbatar musu da cewa matsalolin masu wucewa ne.

Rahoto daga Wakilin Tsinkaya a Gidan Gwamnati.

posted from Bloggeroid

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home